Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato 'dan'uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al'amarin jiki da kuma wajen al'amarin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:16
10 Iomraidhean Croise  

Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.


Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”


Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, 'yantacce ne na Ubangiji. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu.


Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.


Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su. Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.


Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,


Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan