Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Amma ba na so in yi kome ba tare da yardarka ba, don kada alherinka yă zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:14
10 Iomraidhean Croise  

Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.


A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.


Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan.


Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?


Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


Saboda haka, na dai ga lalle ne in roƙi 'yan'uwan nan su riga ni zuwa a gare ku, su tanada baiwar nan da kuka yi alkawari kafin in zo, domin a same ta a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.


Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan