Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Dā kam sona in riƙe shi a wurina, yă riƙa yi mini hidima a madadinka, muddin ina ɗaure saboda bishara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:13
8 Iomraidhean Croise  

Na yi farin ciki da zuwan Istifanas, da Fartunatas, da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku.


Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai,


Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.


Daga Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu, da kuma Timoti ɗan'uwanmu, zuwa ga Filiman ƙaunataccen abokin aikinmu,


ina roƙonka saboda ɗana Unisimas, wanda na zama ubansa ina ɗaure.


Ga shi nan, na komo maka da shi kamar gudan zuciyata.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan