Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.
Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.
Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.
“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’