Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.
Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.