Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ya Ubangiji kunya ta rufe mu, mu da sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, saboda mun yi maka zunubi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:8
15 Iomraidhean Croise  

saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”


duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’


ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu'ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra'ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra'ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.


Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.


Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.


Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.


In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


“Mun yi zunubi, mun tayar, Kai kuwa ba ka gafarta ba.


Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!


domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.


Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan