Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:5
31 Iomraidhean Croise  

Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.


saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”


Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.


Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi, Mugaye ne, mun aikata mugunta.


Ban raina koyarwarka ba Saboda kai ne ka koya mini.


Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya, Ka zo ka neme ni, ni bawanka, Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.


Na yi biyayya da umarnan Ubangiji, Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.


Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.


wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.


Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.


Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


domin mutanen da suke cikinsu sun aikata mugayen abubuwa da suka tsokane ni. Sun miƙa wa gumaka hadayu, suka kuma bauta musu, ko da yake su, ko ku, ko kakanninku, ba ku san su ba.


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.


“Mun yi zunubi, mun tayar, Kai kuwa ba ka gafarta ba.


Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.


Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.


Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.


“Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta.


Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa.


Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”


Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’


Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan