Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:25
32 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.


An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.


Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,


Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.


Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.


Ya yi magana a gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”


Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.


A cikin kwana hamsin da biyu aka gama garun, ran ashirin da biyar ga watan Elul.


Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni, Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.


Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.


Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai, Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.


Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”


Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki.


Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Ki tattara sojojinki, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila da sanda.


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”


“Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),


“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe.


Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”


kuka kuwa kashe Tushen Rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka.


Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.


Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”


Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan