Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:24 - Littafi Mai Tsarki

24 “An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:24
50 Iomraidhean Croise  

Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra'ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra'ila.


Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.”


Kana ƙaunar abin da yake daidai, Kana ƙin abin da yake mugu. Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka, Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.


Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”


Ku duba sammai, ku duba duniya! Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi, Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa, Dukan mutanenta kuma za su mutu. Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.


Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata za ta kasance har abada abadin.”


Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina.


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare, Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba. Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom, Zai tone zunubanki.


“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!


Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila.


Sa'ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba'in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.


Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba'in da tara a gare su.


Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa.


Sa'an nan ya ce, “Waɗannan su ne keɓaɓɓu biyu waɗanda yake tsaye kusa da Ubangijin dukan duniya.”


Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.


Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”


Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.


Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,


yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Mala'ikan ya amsa mata ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.


Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.


Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe.


Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.


Amma ku kuka ƙi Mai Tsarkin nan, mai adalci kuka roƙa a saukar muku da mai kisankai,


Musa ma ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni. Lalle ne ku saurari duk abin da ya faɗa muku.


Sarakunan duniya sun kafa dāga, Mahukunta kuma sun haɗa kai, Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’


In kuwa tun muna maƙiyan Allah aka sulhunta mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da yake an sulhunta mu, ashe kuwa, za a fi kāre mu ta wurin rayuwarsa ke nan.


Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.


da nufin ta wurinsa, Allah yă sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na sama, yana ƙulla zumunci ta wurin jininsa na gicciye.


ya kuma yanke igiyar nan ta Shari'a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa.


Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.


Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.


Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai.


In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan