Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:2 - Littafi Mai Tsarki

2 a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:2
32 Iomraidhean Croise  

don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba'in, ta kiyaye asabatai.


Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.


Umarnanka suna faranta mini rai, Su ne mashawartana.


Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.


Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,


Urushalima, da biranen Yahuza, da sarakunanta, da shugabanninta, za su zama kango da abin ƙyama da abin raini, da abin la'ana. Haka yake a yau.


“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’


Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.


“Ubangiji ya ce, ‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.


Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”


Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!


Mutum ko dabba ba zai ratsa ta cikinta ba. Za ta zama kufai har shekara arba'in.


Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, har yaushe za ka ƙi nuna jinƙai ga Urushalima da biranen Yahuza, waɗanda kake jin haushinsu shekara saba'in ke nan?”


in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa'ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba'in, saboda ni ne kuka yi azumin?


“Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),


“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


Sai bābān ya ce wa Filibus, “Shin kam, annabin nan, maganar wa yake yi? Tasa ko ta wani?”


Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa.


Albarka tā tabbata ga mai karanta maganar nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma suke kiyaye abin da yake a rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan