Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ya Ubangiji, saboda dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hasalarka da ka yi da birninka Urushalima, tsattsarkan tudunka. Gama saboda zunubanmu da muguntar kakanninmu, Urushalima da jama'arka sun zama abin ba'a ga waɗanda suke kewaye da mu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:16
33 Iomraidhean Croise  

Ka iske shi amintacce a gare ka, Ka kuwa yi masa alkawari. Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana, Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa, Ta zama inda zuriyarsa za su zauna. Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.


Ya Ubangiji ka ji addu'ata, Ka kasa kunne ga roƙona! Kai adali ne mai aminci, Don haka ka amsa mini!


Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni. Kada ka bari a yi nasara da ni. Kai Allah mai adalci ne, Ka cece ni, ina roƙonka!


Bari mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila. Ku yabe shi yanzu da har abada! Amin! Amin!


Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni. Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!


Sauran al'ummar da take kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.


Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka daina jin haushinmu!


Ya Ubangiji, kada ka manta da yadda maƙiyanka suka ci mutuncin zaɓaɓɓen sarki da ka naɗa! Suka yi ta cin mutuncinsa duk inda ya tafi.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.


Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.


Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.


Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.


Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.


Ka yi laifi saboda ka zubar da jini, ka ƙazantar da kanka da gumakan da ka yi. Saboda haka ka matso da lokacinka kusa, ƙayyadaddun shekarunka sun cika. Domin haka na maishe ka abin zargi ga sauran al'umma, da abin ba'a ga dukan ƙasashe.


Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al'ummai da suke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.


Zai kafa manyan alfarwai na sarauta a tsakanin teku da tsattsarkan dutse. Amma zai mutu ba kuwa wanda zai taimake shi.”


Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna.


“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.


Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.


domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,


In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.


Yakan sa waɗansu mutane su zama matalauta, Waɗansu kuwa attajirai. Yakan ƙasƙantar da waɗansu, Ya kuma ɗaukaka waɗansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan