Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:15
30 Iomraidhean Croise  

Gama su jama'arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.


saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”


duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’


“Su bayinka ne, mutanenka ne kuma, waɗanda ka fansa da ikonka.


ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu'ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra'ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra'ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.


Ka kuma aikata alamu da al'ajabai a kan Fir'auna, Da fadawansa duka, da mutanen ƙasarsa, Gama ka san yadda suka yi wa jama'arka danniya. Ta haka ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.


Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta, Domin ya nuna ikonsa mai girma.


In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.


Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”


Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.


Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.


Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”


Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”


Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.


Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.


Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu, Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa. Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada, Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”


Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.


Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.


Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni.


“Mun yi zunubi, mun tayar, Kai kuwa ba ka gafarta ba.


Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.


“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.


Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’


Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’


Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.


Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan