Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Domin haka Ubangiji ya shirya bala'i, ya kuma aukar mana da shi, gama Ubangiji Allahnmu mai adalci ne cikin dukan abin da ya aikata, amma mu ba mu bi maganarsa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:14
16 Iomraidhean Croise  

Sai sarakunan Isra'ila tare da sarki Rehobowam, suka ƙasƙantar da kansu, suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”


Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”


Ka yi daidai da ka hukunta mu haka! Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.


Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne. Dukan umarnansa, abin dogara ne.


Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri, Allahnmu mai rahama ne.


Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, Dokokinka kuma daidai ne,


Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona, Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.


Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure.


Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?


Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.


Za su kewaye Yahuza kamar masu tsaron saura, Saboda ta tayar wa Ubangiji.’ Ni Ubangiji na faɗa.


Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.


Maƙiyanta sun zama shugabanninta, Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta. Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahala Saboda yawan zunubanta. 'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.


Da yake ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan