Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk da haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:13
35 Iomraidhean Croise  

‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,


“Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu, Suna tanada wa kansu fushi, Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su.


Ka buɗe idona Domin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.


Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka, In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.


Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya, Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.


Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka daina jin haushinmu!


Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.


Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma faruwa.”


Ubangiji ya ce, “Amma ba ni kuka yi wa sujada ba, Kun gaji da ni, ya Isra'ila.


Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.


Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu'a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.


Jama'ar Isra'ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.


Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki.


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, ‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna.


Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.”


Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.


Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.


Ya Ubangiji, ka komo da mu zuwa gare ka! Mu kuwa za mu koma. Ka sabunta kwanakinmu su zama kamar na dā.


Da yake ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”


Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.


Girmankan mutanen Isra'ila ya kai ƙararsu, Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu, Ba su kuwa neme shi ba.


Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.


“Dukansu suna da zafi kamar tanderu. Suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sun faɗi. Ba wanda ya kawo mini kuka.”


Sa'an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai,


To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),


A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.


Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.”


in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take.


Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.


In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan