Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:7
8 Iomraidhean Croise  

Sarkin kudu zai husata ya kai wa sarkin arewa yaƙi, za a ba da rundunar sojojin sarkin arewa a hannunsa.


Sauran dabbobi kuwa aka karɓe mulkinsu, amma aka bar su da rai har wani ƙayyadadden lokaci.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Ya ƙasaita, har ya kai cikin rundunar sama. Ya jawo waɗansu taurari zuwa ƙasa, ya tattake su.


Sai ya zo wurin ragon, mai ƙahoni biyu, wanda na gani a tsaye a gāɓar kogi. Bunsurun kuwa ya tasar masa da fushi mai zafi.


Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.


Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba.


Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan