Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sa'ad da nake cikin tunani, sai ga bunsuru ya ɓullo daga wajen yamma, ya ratsa dukan duniya, ba ya ko taɓa ƙasa. Akwai ƙaho na gaske a tsakanin idanunsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Yayinda nake tunani game da wannan, farat ɗaya sai ga bunsurun da yake da sanannen ƙaho tsakanin idanunsa ya ɓullo daga wajen yamma, yana ratsa dukan duniya ba ya ko taɓa ƙasa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:5
7 Iomraidhean Croise  

“Sa'an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama.


An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.


A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.


“Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.


Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da yake tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko.


Sai ya zo wurin ragon, mai ƙahoni biyu, wanda na gani a tsaye a gāɓar kogi. Bunsurun kuwa ya tasar masa da fushi mai zafi.


Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan