Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:3
25 Iomraidhean Croise  

Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa'an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.


Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza.


Mutanen kuwa suka yi ijara da mashawarta, da za su sa niyyarsu ta shiririce tun daga zamanin Sairus, Sarkin Farisa, har zuwa zamanin Dariyus, Sarkin Farisa.


A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya yi biki saboda sarakunansa, da barorinsa, da sarakuna yaƙin Farisa da Mediya, da manyan mutane, da hakiman larduna.


Ubangiji ya ce “Ina zuga mutanen Mediya, don su faɗa wa Babila da yaƙi. Ba su kula da azurfa ba, ba kuwa za a jarabce su da zinariya ba.


Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa. Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.


Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina, Za ka yi abin da nake so ka yi, Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima, A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”


Ku wasa kibau, ku cika kwaruruwanku! Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan Mediyawa, Domin yana niyyar hallaka Babila. Gama Ubangiji zai yi ramuwa saboda Haikalinsa.


Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa.


A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.


Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.


Daniyel kuwa ya bunƙasa a zamanin mulkin Dariyus da na Sairus mutumin Farisa.


“Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’


A wahayin sai na gani ina a bakin kogin Ulai a Shushan, masarautar lardin Elam.


“Ragon nan mai ƙaho biyu da ka gani, sarakunan Mediya ne da na Farisa.


Da na ɗaga idona, sai na ga ƙahoni huɗu.


Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo.


Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.


Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”


Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama.


Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne.


ya ta da idanunsa ya ga Isra'ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa.


Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”


Sa'an nan na ga wata dabba na fitowa daga cikin ƙasa. Tana da ƙaho biyu kamar na ɗan rago, maganarta kuwa kamar ta macijin nan.


Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan