Daniyel 8:27 - Littafi Mai Tsarki27 Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202027 Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata. Faic an caibideil |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.