Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:25
21 Iomraidhean Croise  

Sukan mutu nan da nan, Da tsakar dare manya da ƙanana sukan shuɗe farat ɗaya, An kawar da su ba da hannun mutum ba.


“Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.


Gama zunubin mutanena Ya fi zunubin Saduma, Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.


Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce.


Zai kafa manyan alfarwai na sarauta a tsakanin teku da tsattsarkan dutse. Amma zai mutu ba kuwa wanda zai taimake shi.”


Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari'a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Nan take sai mala'ikan Ubangiji ya buge shi don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.


Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan.


A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.


Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”


Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan