Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:23 - Littafi Mai Tsarki

23 “A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:23
23 Iomraidhean Croise  

A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”


don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.


Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.’ ”


Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.


Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”


“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.


Ba zato ba tsammani zai kai wa lardi mafi arziki hari. Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba wa mabiyansa kwason yaƙi, da ganima, da dukiya. Zai kuma yi shiri ya kai wa kagara hari amma domin ɗan lokaci ne kawai.


“Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone.


Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.


Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.


Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.


Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.


Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim, Za su wahalar da Assuriya da Eber, Su kuma da kansu za su lalace.”


To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!


al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara.


suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.


To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan