Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:22
8 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.


“Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da yake tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko.


“A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.


Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya.


Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.


Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan