Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:19
15 Iomraidhean Croise  

Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona, Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai, Wannan shi ne lokacin!


Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


“A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.


Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.


Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama'an nan.


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.


Al'ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko, Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari'a, A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba, A kuma hallaka masu hallaka duniya.”


Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.


domin Allah ya nufe su da zartar da nufinsa, su zama masu ra'ayi ɗaya, su bai wa dabbar nan, mulkinsu, har a cika Maganar Allah.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan