Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Ya ce mini, “Sai an yi kwana dubu biyu da ɗari uku, sa'an nan za a mai da wuri mai tsarki daidai da yadda yake a dā.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:14
14 Iomraidhean Croise  

ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.


Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.


Ni Ubangiji, zan kuɓutar da dukan zuriyar Yakubu, Za su kuwa yi yabona.”


“Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in.


Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar.


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.


Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”


A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.


An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba'in da biyu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan