Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 8:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 8:1
11 Iomraidhean Croise  

A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


A waɗannan kwanaki, ni Daniyel, ina fama da baƙin ciki har mako uku.


Ni kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da suke tare da ni ba su ga wahayin ba, sai dai babbar razana ta auko musu, har suka gudu, suka ɓuya.


Sa'ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.


A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa.


“Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.


“Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”


Sa'ad da ni Daniyel, na ga wahayin, ina so in gane, sai ga wani kamar mutum ya tsaya a gabana.


A wahayin sai na gani ina a bakin kogin Ulai a Shushan, masarautar lardin Elam.


a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan