Daniyel 7:9 - Littafi Mai Tsarki9 “Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20209 “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Faic an caibideil |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.