Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:8
15 Iomraidhean Croise  

Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru, Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!


“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.


“Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.


Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.


Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka,


Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,


Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.


Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.


Kamannin fārin nan kuwa kamar dawakai ne da suka ja dāgar yaƙi, a kansu kuma da wani abu kamar kambin zinariya, fuskarsu kuwa kamar ta mutum,


Kada ku ƙara yin magana ta girmankai, Ku daina maganganunku na fariya, Gama Ubangiji Allah shi ne masani, Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan