Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:5
14 Iomraidhean Croise  

Elisha ya waiga, ya gan su, ya la'anta su da sunan Ubangiji. Sai waɗansu namomin jeji guda biyu suka fito daga cikin kurmi suka yayyage arba'in da biyu daga cikin samarin.


Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.


Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji.


“Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.


A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.


Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”


Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


“Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.


Zan auka musu kamar beyar, Wadda aka ƙwace mata 'ya'ya. Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki, Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.


Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan