Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:28 - Littafi Mai Tsarki

28 “Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 “Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:28
19 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”


'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.


Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.


Aka bar ni, ni kaɗai, na ga wannan babban wahayi, ni kuwa ba ni da sauran ƙarfi. Fuskata ta sauya, ta turɓune, ba ni da sauran ƙarfi.


Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.


“Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”


Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.


A raba shi da hankali irin na mutane, A ba shi irin na dabba. Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.


Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.


Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.


“Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.


A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.


Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki. Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”


Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.


Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.


Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ɗungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi.


Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.


Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.


“Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan