Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:27
29 Iomraidhean Croise  

Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada.


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa, Dukan sauran al'umma za su bauta masa!


Dukan sauran al'umma da ka halitta Za su zo su rusuna har ƙasa a gabanka. Za su yabi girmanka,


Al'ummai da yawa za su taimaki jama'ar Isra'ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al'umma za su yi wa Isra'ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra'ilawa a dā yanzu Isra'ilawa za su kama su. Jama'ar Isra'ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.


Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe, Jama'arki za su karɓi ƙasarsu Wadda al'ummai suke mallaka yanzu, Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, “Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.


Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”


Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.


sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari'a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.


Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.


A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.


Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada, Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”


Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”


Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko.


Sa'an nan aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce mini, “Tashi ka auna Haikalin Allah, da bagadin hadaya, da kuma masu sujada a ciki,


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”


Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.


Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.


Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan