Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa'an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:24
13 Iomraidhean Croise  

“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.


Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.


Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.


“Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.


Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.


Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.


Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan