Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:23 - Littafi Mai Tsarki

23 “Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 “Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:23
5 Iomraidhean Croise  

Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki.


sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari'a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.


Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa'an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan