Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:20
9 Iomraidhean Croise  

“Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone.


“Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.


“Ina dubawa ke nan sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka har ya rinjaye su,


“Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan