Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:19 - Littafi Mai Tsarki

19 “Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:19
4 Iomraidhean Croise  

Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan