Daniyel 7:14 - Littafi Mai Tsarki14 Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202014 Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa. Faic an caibideil |
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.