Daniyel 7:11 - Littafi Mai Tsarki11 “Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202011 “Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta. Faic an caibideil |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.