Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Kogin wuta yana gudu daga gabansa. Dubun dubbai suna ta yi masa hidima, Dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa, Aka kafa shari'a, aka buɗe littattafai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:10
26 Iomraidhean Croise  

Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala'ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa.


Sai Mikaiya ya ce, “Ji maganar Ubangiji, na ga Ubangiji yana zaune a bisa kursiyinsa, dukan rundunan sama suna tsaye dama da shi da hagu da shi.


Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima? Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?


Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a Sama, Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!


Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa, Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.


Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba, Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.


Daga Sinai da dubban manyan karusansa, Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.


Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


“A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.


sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari'a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.


Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari'a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada.


Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa'an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


Ya ce, “Ubangiji ya taho daga Sina'i, Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka, Ya taho tare da dubban tsarkakansa, Da harshen wuta a damansa.


Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?


Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku.


Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,


Al'ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko, Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari'a, A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba, A kuma hallaka masu hallaka duniya.”


Sa'an nan na duba, sai na ji muryar mala'iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan