Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 7:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 7:1
34 Iomraidhean Croise  

Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”


Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.”


Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.


Allah ya faɗa mini in rubuta a littafi yadda mutane suke, saboda ya zama tabbatacciyar shaida a kansu.


Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.


Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.


Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya.


A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.


A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


Nebukadnezzar ya yi mafarki a shekara ta biyu ta sarautarsa, ya kuwa damu ƙwarai har barci ya gagare shi.


Sarki kuwa ya ce wa Daniyel, mai suna Belteshazzar, “Ka iya faɗa mini mafarkin duk da fassararsa?”


“ ‘A cikin wahayin da na gani sa'ad da nake kwance a gado, sai ga wani mai tsaro, tsattsarka, ya sauko daga sama.


Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.


Sarki Belshazzar ya yi wa dubban manyan mutanensa liyafa, ya kuwa sha ruwan inabi a gabansu.


“Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.


A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.


“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


“Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.


“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna, Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.


Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.


Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana.


An tilasta mini ne in yi gadara, ko da yake ba ta amfane ni da kome ba. Amma zan ci gaba da zancen ruya da wahayi da Ubangiji ya yi mini.


To, ka rubuta abubuwan da ka gani, da abubuwan da suke a nan a yanzu, da abubuwan da suke shirin aukuwa bayan wannan.


Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan