Daniyel 6:8 - Littafi Mai Tsarki8 Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20208 Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Faic an caibideil |
Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.
Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?” Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”