Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:5
8 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.


Mugu yakan yi fakon mutumin kirki, Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,


Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu'a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’


Sa'an nan ya ce wa Dawuda, “Ka fi ni adalci, gama ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.


Shugabannin sojojin Filistiyawa suka ce, “Me waɗannan Ibraniyawa suke yi a nan?” Akish kuwa ya ce wa shugabannin sojojin Filistiyawa, “Ai, wannan Dawuda ne baran Saul, Sarkin Isra'ila, wanda yake tare da ni tun da daɗewa. Tun lokacin da ya zo wurina ban taɓa samunsa da wani laifi ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan