Daniyel 6:4 - Littafi Mai Tsarki4 Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20204 A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. Faic an caibideil |