Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:3
12 Iomraidhean Croise  

Ka kula fa, kada ka yi kasala a wannan al'amari, don me ɓarna za ta bunƙasa har ta cuci sarki?”


sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.


Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.


Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.


Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.


To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.


Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”


Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima.


Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan