Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar, Yana aikata alamu da mu'ujizai a sama da duniya. Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:27
23 Iomraidhean Croise  

Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani, Ta wurin tsananin da suke sha, Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.


Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada.


Yakan cece ni daga maƙiyana. Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,


Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara. Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa, Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.


Kai ne maɓoyata, Za ka cece ni daga wahala. Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka, Domin ka kiyaye ni.


Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu, Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!


Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta. Yakan kiyaye rayukan jama'arsa, Yakan cece su daga ikon mugaye.


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”


Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”


kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”


sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan