Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:24
13 Iomraidhean Croise  

Amma bai kashe 'ya'yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”


Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa'an nan sarki ya huce.


Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.


Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce, cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.


Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu! Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.


Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.


Ba wanda zai faɗi ƙarya a majalisa ya rasa shan hukunci, maƙaryaci, tasa ta ƙare.


Dare farai na yi ta kuka saboda azaba, Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana. Na zaci Allah zai kashe ni.


Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.


Tsananin umarnin sarki ya sa aka haɓaka wutar, sai harshen wutar ya kashe waɗanda suka jefa su Shadrak, da Meshak, da Abed-nego cikin wutar.


“Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan