Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:23
18 Iomraidhean Croise  

Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama'a.”


Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.


Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”


Na yi biyayya da umarnan Ubangiji, Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.


Yakan taimake su, yă kuɓutar da su, Yakan cece su daga mugaye, Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.


Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra'ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa.


Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.


Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi, Waɗanda suke dogara gare ka.


Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.


Sarki ya ce, “Amma ina ganin mutum huɗu a sake, suna tafiya a tsakiyar wuta, ba kuma abin da ya same su, kamannin na huɗun kuwa kamar na ɗan alloli.”


Sa'ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi.


Sarki ya koma fādarsa, ya kwana yana azumi, bai ci abinci ba, ya kuma kāsa yin barci.


Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”


waɗanda ta wurin bangaskiya suka ci masarautai, suka aikata adalci, suka sami cikar alkawarai, suka rurrufe bakunan zakoki,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan