na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”
Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar.