Daniyel 6:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20202 ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. Faic an caibideil |
Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”