Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”
duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan'uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.
Saboda haka, ni ma da na kasa daurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famarmu kuma yă zama banza.