Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Sarki ya koma fādarsa, ya kwana yana azumi, bai ci abinci ba, ya kuma kāsa yin barci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:18
16 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba.


Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.


A wannan dare kuwa sarki ya kasa yin barci, sai ya umarta a kawo littafin da aka rubuta al'amuran da suke faruwa don tunawa. Aka kuwa kawo, aka karanta wa sarki.


Suna rawa ana kaɗa garaya, Ana busa sarewa.


A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu Muka rataye garayunmu.


Ba ya barina in yi barci, Na damu har na kāsa magana.


Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.


Sun jefa ni da rai a cikin rami, Suka rufe ni da duwatsu.


A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.


Nebukadnezzar ya yi mafarki a shekara ta biyu ta sarautarsa, ya kuwa damu ƙwarai har barci ya gagare shi.


Gari na wayewa, sai sarki ya tashi, ya tafi da gaggawa wurin kogon zakoki.


Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan