Daniyel 6:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202016 Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Faic an caibideil |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.