Daniyel 6:15 - Littafi Mai Tsarki15 Sai waɗannan mutane suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ka sani fa ya sarki, doka ce ta Mediya da Farisa, cewa ba dama a soke doka ko umarni wanda sarki ya kafa.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202015 Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.” Faic an caibideil |
Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?” Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”